16 Yuni 2026 - 11:58
Source: ABNA24
Labarai Cikin Hotuna | Na Gudanar Da Tattaki Juyayin Shahadar Imam Hussain As A Garin Zaria Rana 1

A safiyar yau Talata 16/06/2026 Matasan Cikin Garin Zariya, Sun Futo Muzaharar juyayi, Wanda suke gabatarwa a duk Watan Ashura na ko wacce shekara, inda suke farawa tun daya daya ga wata har zuwa goma ga watan. kaman yanda kuke gani a Hotuna Matasan gasu sun sanya Bakaken riguna don Taya Manzon Rahma Jajen Abun da ya faru da Imam Hussain (AS) a filin Karbala. ‎

Har wala yau a yau Talata  16/06/2026, Zallar matasa daga Tudun Jukun Zariya sun fita jogin ɗin  safe kamar yadda aka saba yi duk shekara a farko watan Muharram.  Yau rana ta yara da manya sun fito suna fadin "labbaika Ya Hussain." 
Madauka Hotuna: Mahadi Media / Muhammad S Abdullahi 
Zaria Media Forum
16/06/2026
 

Your Comment

You are replying to: .
captcha